Isa ga babban shafi
Mexico

Mexico na karbar bakin bakuncin taron takaita cinikin makamai tsakanin kasashe

Wakilan kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniya duniya kan yadda ya kamata a gudanar da cinikin makamai, sun hadu a birnin Cancun na kasar Mexico, inda suke tattaunawa a game da yadda za a tabbatar da cewa yarjejeniyar ta yi domin tabbatar da tsaro a duniya. 

Wasu makamai, irin wadanda ake kokarin takaita yaduwarsu a duniya
Wasu makamai, irin wadanda ake kokarin takaita yaduwarsu a duniya REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Taron na yini uku ya hada wakilai ne daga illahirin kasashen da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya, da kuma yadda ya kamata a gudanar da cinikin makamai, lura da halin da ake ciki na bazuwar makamai da ake amfani da su wajen kashe jama’a a sassan duniya.

A watan Disambar bara ne yarjejeniyar kasa da kasa kan yadda ya kamata a yi cinikin makamai ta fara aiki, bayan da aka sami adadin kasashen da ake bukata su sanya hannu kan yarjejeniyar, to sai dai manazarta na ganin cewa akwai manyan kalubale wajen aiwatar da ita a aikace.

Wata babbar matsalar da ke iya zaman barazana ga wannan yarjejeniya dai, ita ce yadda wasu makamai ke fadawa a hannun ‘yan ta’adda da kuma kungiyoyi masu tayar da kayar baya.

Cinikin makamai dai na daga cikin hanyar da ke samar wa wasu kasashe kudaden shiga, domin kuwa a kowace shekara ana sayar da makaman da kudinsu zai kai Euro Bilyan 80 a kasashen duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.