Isa ga babban shafi
ECOWAS

Kungiyar ECOWAS na shirin aiwatar da dokar hana sanya hijabi

Shugabanin Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS ko CEDEAO a yau alkamis sun soma nazarin aiwatar da dokar hana mata sanya hijabi a bainar jama’a

Taron ECOWAS a Abuja,Najeriya
Taron ECOWAS a Abuja,Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Wannan dai wani yunkuri ne na ganin an kawo karshen anfani da mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake dama dakile ayyukan ta’addanci baki daya a yankin.

Kungiyar Boko Haram dake da tushe a Najeriya ta shahara wajen anfani da mata da a lokuta da dama ke sanye da hijabi a yayin kai hare-haren kunar bakin wake akan jama'a, an sami asarar rayuka da dama a kasashe kamar su Kamarou da Tchadi dama Najeriya sakamakon ire-iren wadannan hare-haren na ta'addanci.

Shugaban kungiyar Kadre Desire Ouedraogo ya sanarwa manema labarai cewa yakamata shugabanin kasashen ECOWAS su aiwatar da dokar hana sanya hijabi a bainar jama’a don baiwa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu na bincike cikin sauki.

Batun haramta sanya Hijabin na zuwa ne a yayin da kungiyar ke kammalla taron ta a Abujan Najeriya,
Shekaru 40 kenan da kafa kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.