Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi ta yi watsi da matakin tura dakaru 5,000

Gwamnatin Burundi ta yi watsi da matakin kungiyar Tarayyar Afrika na tura dakaru 5,000 a cikin kasar domin aikin wanzar da zaman lafiya. Burundi tace bata bukautar wasu dakaru kuma ba zata amince su shigo cikin kasar ba.

Shugaban kasar Burundi  Pierre Nkurunziza.
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza. AFP PHOTO / LANDRY NSHIMIYE
Talla

A ranar Juma’a kwamitin tsaro da zaman lafiya na Tarayyar Afrika ya amince da matakin aikawa da dakaru zuwa Burundi na tsawon watanni 6 domin kare rayukan fararen hula daga rikicin kasar.

Burundi tace a matsayin na halattacciyar gwamnati da aka zaba tana da hakkin a tuntubeta kafin daukar matakin.

Sama da mutane 400 ne dai suka mutu tun barkewar zanga-zangar adawa da matakin shugaba Pierre Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku.

Daruruwa ne kuma suka fice kasar saboda tsoron barkewar yakin basasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.