An sace kanwar Gwamnan Bayelsa
Wasu ‘Yan bindiga sun sace kanwar gwamnan jihar Bayelsa a kudancin Najeriya kamar yadda ‘Yan Sanda suka tabbatar a ranar Lahadi.
Wallafawa ranar:
Jami’an ‘Yan sandan jihar sun ce an sace Nancy Dickson kanwar Gwamnan Bayelsa Seriake Dickson a shagonta tare da wata da ke aiki karkashinta a Yenagoa a ranar Asabar.
'Yan sandan sun ce sun kaddamar da bincike yanzu haka akan ‘Yan bindigar da ba a tantance ba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da gwamna Dickson ke neman sake lashe zaben Bayelsa bayan hukumar zabe tace ba a kamala zaben jihar ba da aka gudanar a ranar 5 ga watan Disemba saboda rikici a yankin Ijaw.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu