Sojin Najeriya sun kwace wani jirgin ruwa shake da Fetir a Bayelsa
Rundunar Sojin ruwan Najeriya tace ta kwace wani jirgin ruwa shake da lita miliyan biyu da dubu dari na danyan man fetur a Jihar Bayelsa, wanda aka sace. Kwamnadan rundunar sojin, Rear Admiral Sidi Ali Hassan Usman ya tabbatar da haka yana mai cewa sun kama mutane 21 da ake zargi da satar man.
Wallafawa ranar:
Satar danyan mai a Najeriya dai ta zama ruwan dare inda tattalin arzikin kasar ya dogara kacokan ga fitar da danyen man.
Rundunar sojin ruwan tace barayin sun gaza gabatar da takardun fitar da danyen mai daga lasisin Kamfanin NNPC kuma babu wani izini da suka samu daga hedikwatar sojin ruwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu