Isa ga babban shafi
Najeriya-Amnesty

Amnesty ta soki Kamfanin Shell game da tsiyayar mai a Najeriya

Hukumar Kare Hakkin bil’adama ta Amnesty International da cibiyar kare Muhalli ta CEHRD, ta zargi kamfanin hako mai na Shell da cewa yana yin makarkashiya game da binciken tsiyayar mai da ke aukuwa a yankin Niger Delta a Kudancin Najeriya.

Les villageois se tiennent près d'un récipient contenant du pétrole, près du village d'Orobiri, quelques jours le déversement de pétrole off-shore,
Les villageois se tiennent près d'un récipient contenant du pétrole, près du village d'Orobiri, quelques jours le déversement de pétrole off-shore, REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Wani sabon rahoto da Amnesty International da tare da hadin gwiwar cibiyar kae muhalli suka fitar sun yi nuni cewa akwai bayanan karya da kamfanin mai na Shell ya fitar game da musabbabin tsiyayar mai a yankin Niger Delta, da kuma yawan man da ke kwarara a yankin.

Bincike ya yi nuni da cewa akwai kurakurai game da musabbin tsiyayar man tare da karkata hankulan mutane zuwa wani batu da ba shi da nasaba da lamarin.

Kungiyar ta kafa da hujjoji da ke nuni da cewa kamfanin Shell ya canja bayanai da dama tana mai cewa akwai bukatar kamfanin ya dauki alhakin biyan diyya ga mutanen yankin tare da kira ga kamfanonin hakar mai da su dinga buga dukkanin sakamakon binciken da suka yi na tsiyayar mai tare da hujjoji masu karfi.

Rahoton yace yankin Niger Delta shi ne yanki a duk fadin duniya da idan aka samu matsalar kwarara Mai, Kamfanonin ke ikrarin cewa ba laifinsu ba ne sabanin wasu yankunan kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.