Burkina na tuhumar Compaore da laifin kisan Sankara
Hukumomi a kasar Burkina Faso sun fitar da sammacin kama tsohon shugaban kasar Blaise Compaore domin tuhumar sa da hannu a kisan da aka yi wa tsohon shugaban kasar Thomas Sankara a 1987.
Wallafawa ranar:
A ranar 15 ga watan Oktoban 1987 aka kashe Shugaba Sankara a juyin mulkin da amininsa Blaise Compoare ya dare kan madafan ikon Burkina Faso.
Yanzu haka Compaore na gudun hijira ne a kasar cote d’Ivoire bayan kaddamar da zanga-zangar da ta yi sanadin hambarar da gwamnatinsa.
Bincike da dama da aka gudanar na bayyana cewa harbe Sankara aka yi.
A yanzu kuma Masharhanta a Burkina Faso na ganin matsin lambar al’ummar kasar ne ya tilastawa gwamnatin rikon kwarya daukar wannan mataki.
Dr Ali Sakulla Jika, malami a jami’ar Ouagadougou, ya ce al’ummar Burkina Faso na ganin hakarsu ba ta cim ma ruwa ba idan har ba a kamo Compoare ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu