Za mu sa ido ga alkawullan Buhari- PDP
Jam’iyyar PDP mai adawa a Tarayyar Najeriya, ta ce za ta zura ido domin ganin yadda gwamnatin Muhammadu Buhari za ta aiwatar da kasafin kudin kasar na badi, wanda shugaban ya gabatarwa ‘yan majalisar kasar a ranar talata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mataimakin sakataren yada labaran PDP Abdullahi Jalo ya ce batun kirkiro da gurabobin ayyukan yi da shugaba Buhari ya yi alkawari, ba wani bakon abu ba ne domin Jam'iyyarsu ce ta soma yin haka.
Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin na Naira Tiriliyon 6.08, wanda ya kunshi kashi 20 na kudaden da gwamnatin za ta kashe.
An ware kudi Naira Biliyan 433.4 ga ayyukan hanyoyi da Wuta da gidaje. Sannan kudi Naira biliyan 202 aka ware wa bangaren Sufuri.
Shugaba Buhari yace kasafin kudin zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu