Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 100 sun kone a Anambra

Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla mutane 100 ne suka kone kurmus sakamakon fashewa da aka samu a wata masana’antar gas a Jihar Anambra a kudancin kasar.

REUTERS/Max Whittaker
Talla

Rahotanni sun ce lamarin ya auku ne a jiya a garin Nnewe bayan gas din da wata babbar mota ta zube a masana’atar suka tarwatse.

Kuma ma’aikatan masana’antar ne da dama suka kone tare da mutanen da suka je domin a cika masu tukunyar gas ta dafa abinci.

Sai dai babu wani tabbaci daga 'Yan Sanda akan adadin mutanen da suka mutu.

Wannan  na zuwa ne a yayin da al’ummar Kirista ke shirye-shiryen bikin Kirsimeti a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.