Isa ga babban shafi
Burundi

Gwamnatin Burundu da 'yan tawaye a Kampala domin tattaunawa

Tawagar gwamnati da ta ‘yan adawa a kasar Burundi yanzu haka tana kan hanyar zuwa Uganda domin shiga tattaunawar sulhu a tsakanin bangarorin biyu karkashin inuwar kungiyar tarayyar Afirka.

Shugaban Uganda Yuweri Museveni da na Burundi Pierre Nkurunziza a fadar Entebbe
Shugaban Uganda Yuweri Museveni da na Burundi Pierre Nkurunziza a fadar Entebbe AFP Photo/Peter Busomoke
Talla

Tun a cikin watan Afrilun da ya gabata ne rikicin siyasa ya kunno kai a tsakanin shugaba Nkurunziza da masu adawa da shi, sakamakon yadda shugaban ya aiwatar da shirinsa na tsayawa takara karo na uku.

Tuni dai wasu manyan hafsoshin sojin kasar suka sanar da kafa kungiyar da za ta yi gwagwarmaya da makamai domin kifar da gwmanatin Pierre Nkurunziza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.