Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumomi sun ce mutane 9 ne suka mutu a hatsari Nnewi

Hukumomi a Najeriya sun ce mutane 9 ne suka mutu sakamakon hatsarin da aka sama a wata cibiyar samar da iskar gaz da ke jihar Anambara a makon da ya kawo karshe, a maimakon sama da mutane dari da aka bayar da labarin cewa sun mutu da farko.

fashewar tanka a Najeriya
fashewar tanka a Najeriya Reprodução de vídeo/AFP
Talla

Mai magana da yawun hukumar agajin gaggauwa ta kasar James Eze, ya ce mutane tara ne suka tabbatar da cewa sun mutu, to sai dai a ranar juma’a da ta gabata, shugaban kasar Muhammadu Buhari da kansa, ya ce adadin wadanda suka hallaka a lamarin yak ai gommai.

Lamarin dai ya faru ne a jajibirin Kirismeti, inda rahotanni suka yi nuni da cewa adadin mamatan ya haure dari daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.