An rufe rijistar ‘Yan takarar shugaban kasa a Nijar
Hukumar zabe a Jamhuriyar Nijar ta kammala karbar takardun ‘yan takarar da ke neman kujerar shugaban kasa a zaben da za a yi a ranar 21 ga watan Fabrairun 2016.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Cikin wadanda suka gabatar da takardunsu sun hada da shugaba mai ci Mahamadou Issofou da shugaban ‘yan adawa Seyni Oumarou, da tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane da tsohon shugaban Majalisar dokoki Hamma Amadou wanda yanzu haka ke tsare a gidan yari.
Ma’aikatar cikin gida ne ta karbi takardun inda zata mikawa kotun tsarin mulki domin tantance ‘yan takarar kafin ranar zaben.
An shafe lokaci, Mahamadou Issoufou da Seini Oumarou da Mahamane Ousmane suna yin tasiri a siyasar Nijar.
Sauran manyan ‘yan takarar shugaban kasar sun hada da tsohon Firamnista Amadou Boubakar Cisse da tsohon Ministan noma Abdou Labo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu