Isa ga babban shafi
Nijar

Sojojin Nijar 6 sun mutu bayan sun taka nakiya a Diffa

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar sun ce sojojin kasar shida ne suka rasa rayukansu bayan motarsu ta sintiri ta taka nakiya a yankin Diffa da ke gabashin kasar da ke fama da hare haren kungiyar Boko Haram.

Sojojin Nijar suna karbar horo a yankin Diffa
Sojojin Nijar suna karbar horo a yankin Diffa REUTERS
Talla

Malam Abba Wasiri wani mazauni yankin da aka kai harin yace a ranar Asabar ne al’amarin ya faru a kusa da kauyen Kabalewa.

Sojojin na cikin budaddiyar mota kirar Toyota ne suka taka nakiyar a yayin da suke aikin tsaro tsakanin Bosso zuwa Kabelewa.

Kafar talabijin ta Sahel ta tabbatar mutuwar sojojin Nijar shida tare da wasu biyar da suka samu raunuka.

‘Yan Boko haram dai sun dade suna addabar yankin Diffa da ke cikin dokar ta-baci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.