Isa ga babban shafi
Nijar

An rufe makarantu 150 a jihar Diffa saboda rikicin Boko Haram

Ofishin kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce daga watan fabarairun da ya gabata zuwa yau sama da mutane dubu 47 ne suka bar garuruwansu a jihar Diffa da ke gabashin jamhuriyar Nijar sakamakon tsanantar ayyukan Boko Haram.

Sansanin 'yan gudun hijra a Diifa Jamhuriyar Nijar
Sansanin 'yan gudun hijra a Diifa Jamhuriyar Nijar © Katy Thiam/OCHA Niger
Talla

A rahoton da ta fitar dangane da halin da ake ciki a yankin, Majalisar ta nuna cewa yara sama da dubu 12 ne suka daina zuwa makarantun Boko a jihar sakamakon tsanantar ayyukan Boko Haram a yankin.

A jimilce dai makarantu 150 ne aka rufe mafi yawansu a garurwan da ke gaf da tafkin Chadi da kuma kogin Komadugu Yobe wanda shi ne iyakar Nijar da Najeriya a yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.