Isa ga babban shafi

Janar Itno da Masra sun yi alkawarin lashe zaben Chadi

Janar Mahamat Idriss Deby Itno, Shugaban majalisar sojin Chadi, a wani lokaci da ya ke gudanar da yakin zabensa a yau asabar a Djamena ya dau alkawalin lashen zaben a zagayen farko.

Dan takara kuma shugaban majalisar sojin Chadi Mahamat Idriss Deby.
Dan takara kuma shugaban majalisar sojin Chadi Mahamat Idriss Deby. © AP - Michel Euler
Talla

Yayinda Firaminista da Shugaban majalisar sojin Chadi ya nada, Succes Masra, da ke magana a gaban dubban magoya bayansa a babban birnin kasar N'Djamena, ya bayyana cewa ya na da yekinin lashe zaben a zagayen farko a gaban shugaban majalisar sojin kasar mai shekaru  40 a duniya.

 Succes Masra, firaminista kuma dan takara a zaben Chadi
Succes Masra, firaminista kuma dan takara a zaben Chadi © Denis Sassou Gueipeur / AFP

Janar Mahamat Idriss Deby Itno ya hau karagar mulkin kasar ta Chadi ne  a ranar 20 ga Afrilu, 2021 bayan rasuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno, wanda 'yan tawaye suka kashe bayan ya shafe shekaru 30 yana mulkin kasar ta Chadi.

Chadi na daya daga cikin kasdashen yankin Sahel mafi talauci a duniya.

Janar Mahamat Idriss Déby shugaban majalisar soji kuma dan takara , a Ndjamena,
Janar Mahamat Idriss Déby shugaban majalisar soji kuma dan takara , a Ndjamena, AFP - DENIS SASSOU GUEIPEUR

Wasu daga cikin yan siyasa musaman bangaren adawa na kira ga yan kasar da su kaucewa zaben sabili da zargin Firaminista Succes Masra da aiki da sojoji masu mulki.

Ga baki daya hankula sun karkata ga yan takaran biyu daga cikin yan takara 10 da ake da su a wannan zabe na kasar Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.