'Yan takara 10 ne za su kara a zaben shugaban kasa a Chadi
‘Yan takara goma ne za su kara da juna a zaben shugabancin kasar Chadi da za a gudanar ranar 6 ga watan Mayu mai zuwa, da suka hada maza 9 da kuma mace daya.
Wallafawa ranar:
Ten candidates to run for May 6 presidential elections
Daya daga cikin wadanda za su tsaya takarar akwai Mahamat Idriss Déby da aka fi sani da Kaka wanda ke rike mukamin shugaban rikon kwaryar kasar.
Farkon hawansa karagar Mulki dai ya yi alkawarin ba zai tsaya takarar ba, sai gashi sunan sa na cikin wadanda suka tsaya, Janar Deby dai Soja ne da ya samu horo a kasar sa Chadi da kuma Faransa, sannan yana da mata uku da yara masu yawa.
Sai Firaministan sa Succès Masra, ya na daya daga cikin ‘yan takarar, wanda a can baya shi ne babban dan adawa ga gwamnatin sojin kasar.
Sakamakon wannan adawar ta shi ce ta sa aka kore shi daga kasar amma a shekarar da ta gabata Deby ya dawo da shi kuma ya ba shi mukamin firaminista a watan janairun shekarar nan ta 2024.
Sauran ‘yan takarar sun hada da Alladoum Djarma Baltazar, da Théophile Bongoro Bebzouné, da Nasra Djimasngar, da Mansiri Lopsikreo, da Albert Pahimi Padacké, da Yacine Abdramane Sakine da kuma wata mace guda daya Lydie Beassemda
Kotun kundin tsarin mulkin kasar ta cire sunayen Nassour Ibrahim Neguy Koursum da Rakhis Ahmat Saleh bisa samun su da aikata ba daidai ba.
Yaya Dillo, ya kasance babban dan hamayya ne a kasar kafin sojojin kasar su kashe shi a watan Febrirun shekarar nan a shelkwatar jam’iyyar sa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu