Boko Haram: Nijar ta kafa dokar ta baci a Diffa
Gwamantin Jamhuriyar Nijar ta kafa dokar ta baci a yankin Diffa inda kungiyar Boko Haram ta kashe akalla mutane 40 a 'yan makwannin da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Dokar ta kwanaki 15 za ta bai wa hukumomin kasar damar karfafa matakan tsaro da hana fita da kuma taikata zirga-zirgar mutane da kuma hana safarar kayayyakin abinci kamar yadda gwamnatin ta sanar ta kafar talabijin.
Gwamantin dai ta dau irin wannan matakin a watan Fabairun da ya gabata.
Akalla ‘yan gudun hijira dubu 150 da rikicin Boko Haram a Najeriya ya tilasta wa kauracewa gidajensu, suka samu mafaka a yankin Diffa, yayinda a cikin watanni 8 da suka gabata, kungiyar ta kai hare hare sau 57 a yankin kamar yadda wata kididdigar ta Majalisar dinkin duniya ta nuna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu