An kai hare haren bama-bamai a Maiduguri
Rahotanni daga birnin Maiduguri dake jihar Borno a Najeriya na cewa, an kaddamar da jerin hare haren bama-bamai a birnin tare da kashe mutane da dama kamar yadda mazauna yankin da kungiyar bada agaji ta Red Cross suka sanar.
Wallafawa ranar:
An dai kai hare haren ne a daren jiya talata a yankin Ajilari, inda aka kai munanan hare hare a cikin watan satumban da ya gabata, da ya hada da na ranar 20 ga watan,wanda ya kashe mutane akalla 117.
An dai dora alhakin kai wancan harin akan mayakan Boko Haram da ke ci gaba da kai farmaki kan fararan hula a yan kwanakin nan.
A cikin watan da ya gabata ne kungiyar kare hakkin adam ta Amnesty International ta ce, rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 1 da 600 tun daga watan Yunin da ya gabata a Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru.
Amnesty dai ta bukaci hukumomi da su dauki matakan kare lafiyar farararn hula da hare haren ke ritsa wa da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu