Isa ga babban shafi

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da dokar hukuncin kisa ga dillalan kwaya

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da kudirin dokar da ya bukaci hukuncin kisa kan masu safarar miyagun kwayoyi a kasar.

Zauren Majalisar Dattijan Najeriya, yayin wani zaman 'yan majalisar.
Zauren Majalisar Dattijan Najeriya, yayin wani zaman 'yan majalisar. © dailytrust
Talla

Wannan ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitocin da ke kula da harkokin shari’a, ‘yancin dan Adam, dokar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar.

Shugaban kwamitin shari’a da ‘yancin dan adam, Sanata Mohammed Monguno daga jihar Borno ta Arewa, shine ya gabatar da rahoton yayin zaman majalisar na ranar Alhamis.

Kudirin dokar wanda ya tsallake karatu na uku, na da nufin sabunta dokar haramta amfani da magunguna masu hadarin gaske, da karfafa ayyukan hukumar ta NDLEA, da kuma ba da damar kafa cibiyoyi masu dauke da dakunan gwaje-gwajen muggan kwayoyi.

Sashi na 11 na dokar dai ya tanadi hukuncin daurin rai da rai ga masu fataucin miyagun kwayoyi da kotun da abun ya shafa ta same su da laifin, amma daga bisani kuma lissafi ya sauya bayan neman a mayar da hukuncin zuwa na kisa.

Ko da yake rahoton bai bayar da shawarar yanke hukuncin kisa kan laifin ba kai tsaye, a yayin da ake nazartar kudirin, Sanata Ali Ndume ne ya bukaci a daukaka hukuncin daurin rai da rai zuwa hukuncin kisa, domin hakan ya kasance izina ga masu yunkruin aikata danyen laifin.

A yayin da aka yi la'akari da sadarorin da ke cikin kudirin, mataimakin shugaban majalisar dattawan, Barau Jibrin, wanda ya jagoranci zaman, ya buga gudumarsa, bayan dukkanin mambobin kwamitin sun amice da shawarar Sanata Ali Ndume.

Sai dai Sanata Adams Oshiomhole daga jihar Edo ta Arewa, ya ce bai kamata a yi gaggawar amincewa da irin wannan shawara da ke dauke da batun hukuncin kisa a ciki ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.