Isa ga babban shafi

Ƴan bindiga sun kai hari jami'ar CUSTEC a jihar Kogi tare da sace tarin ɗalibai

Ƴan bindiga a Najeriya sun sake kai hari kan  jami’ar kimiyya da fasaha ta CUSTEC da ke jihar Kogi ta tsakiyar kasar tare da sasce wani adadi mai yawa na ɗalibai, duk da cewa har yanzu mahukuntan kasar basu tabbatar da faruwar wannan farmaki ba.

'Yan bindiga sun addabi jihohin arewacin Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihohin arewacin Najeriya © dailypost
Talla

A cewar wasu shaidun gani da ido ƴan bindigar sun yi dirar mikiya a jami’ar ta CUSTEC da ke yankin Osara a garin Okene ne da misalin karfe 9 na daren jiya Alhamis, kuma har yanzu ba a gama tantance yawan daliban da suka sace ba.

Bayanai sunce harin ƴan bindigar ya faru ne a dai dai lokacin da dalibai suka tattaru a dakunan daukar jarabawa don yin nazarin karatuttukansu dai dai lokacin da jarabawa ke karatowa.

Wani ganau ya ce ƴan bindgar kwatsam suka bayyana daga dazukan da ke zagaye da makarantar tare da fara harbin isaka bayan sun yi wa jami’ar ƙawanya.

A cewar majiyoyi da farko ƴan bindgar sun tattara daliban a dakunan jarabawa gabanin fara tisa keyarsu don shiga cdaji dasu, gabanin isowar jami’an tsaron sa kai wadanda suka yi hadin gwiwa da jami’an tsaron makarantar don tunkarar ƴan bindigar.

Majiyoyin sun ce jami’an tsaron sun yi nasarar daƙile yawan ɗaliban da ƴan bindigar suka ɗiba.

A ranar 13 ga watan nan ne jami’ar ta kimiyya da fasaha a jihar Kogi ke shirin fara jarabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.