Isa ga babban shafi

Rwanda ta musanta zargin hannu a harin sansanin ƴan gudun hijira a Congo

Rwanda ta yi watsi da zargin da Amurka ta  yi mata cewa dakarunta na da hannu a mummunan harin da aka kai wani sansanin ƴan gudun hijira a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyyar Congo.

Shugaban Rwanda Paul Kagame.
Shugaban Rwanda Paul Kagame. AFP - AMANUEL SILESHI
Talla

Majiyoyi a birnin Goma na gabashin ƙasar sun ce aƙalla mutane 9 ne suka mutu bayan da aka kaai wani harin bam a sansanin ƴan gudun hijira da ke wajen birnin.

A wani  saƙo da ya wallafa a shadfinsa na X, kakakin gwamnatin Rwanda, Yolande Makolo ya bayyani wannnan zargi a matsayin mara tushi, yana ma bayyana mamakin yadda masu zargin suke tunanin za ta bada goyon baya a kai hari sansanin ƴan gudun hijira.

Tun da farko ma’aikatar tsaron Amurka ta caccaki abin da ta kira hari daga dakarun Rwanda tare da hadin gwiwar ƴan tawayen M23 a sansanin ƴan gudun hijira na Magungu.

Ita ma gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyyar Ccongo ta bakin kakakinta, Patrick Muyaya, dakarun Rwanda da ƴan tawayen M23 ta ke zargi da kai wannan hari, kamar yadda wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.