Isa ga babban shafi

Rwanda ta yi watsi da kiran Amurka na janye sojojinta daga Congo

Hukumomi a Rwanda sun yi watsi da kiran da Amurka ta yi na neman ta janye sojojinta da makamai a gabashin Congo, inda suka ce aikin kare iyakokin kasar suka yi, a dai-dai lokacin da Congo ke gudanar da wani gagarumin aikin soja a kusa da iyakar.

Hukumomi a Rwanda sun yi watsi da kiran da Amurka ta yi na neman ta janye sojojinta da makamai a gabashin Congo.
Hukumomi a Rwanda sun yi watsi da kiran da Amurka ta yi na neman ta janye sojojinta da makamai a gabashin Congo. © AFP
Talla

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Rwanda ta fitar, na zaman martani ne game da barazanar tsaron da kasar ke fuskanta, daga wajen kungiyar FLDR mai dauke da makamai a Congo, wacce mambobinta suka hada da wadanda ake zargi da aikata kisan kiyashi a shekarar 1994.

Duk da ya ke Rwanda ta dade tana yin tsokaci kan barazanar da kungiyar ta FLDR ke yi, amma hukumomi ba su taba amince wa da kasancewar sojojinta a yankin gabashin Congo ba, wadanda hukumominta ke zargi da goyon bayan kungiyar 'yan ta'addar M23.

Dama a ranar Asabar da ta gabata ne ma’aikatar kula da harkokin wajen Amurka, ta fidda wata sanarwa da ke nuna damuwa kan ayyukan da kungiyar M23 da ta ce ke samun goyon bayan Rwanda, don haka ta bukaci Rwandan ta janye dukkanin sojojinta da ke Congo da kuma makaman da ta girke.

Tun da farko dama dai, kwararru na Majalisar Dinkin Duniya, sun ce suna da kwararan hujjojin da ke tabbatar da cewar sojojin Rwanda na gudanar da ayyukansu ne tare da samun goyon bayan mayakan M23.

A cikin shekarun baya-bayan nan, ayyukan mayakan kungiyar M23 sun tilasta wa dubban mutane barin gidajensu a lardin Arewacin Kivu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.