Isa ga babban shafi
Somalia

Al Shebab ta sake kai mummunan hari a Somalia

Akalla mutane 19 kungiyar Al Shebab ta kashe a wani harin bom da mayakanta guda biyar suka kai a wani wajen cin abinci a birnin Mogadishu da yammacin Alhamis.

Bakin ruwa da ake kira Lido beach da Mayakan Al Shebab suka kai hari a  Mogadishu
Bakin ruwa da ake kira Lido beach da Mayakan Al Shebab suka kai hari a Mogadishu REUTERS/Feisal Omar
Talla

Rahotanni daga Somalia sun ce an kwashe daren jiya ana jin karar harbe harbe da fashe fashe sakamakon harin na mayakan Al Shebab.

‘Yan sanda a Somalia sun ce cikin mutanen da aka kashe sun hada da mata da yara kanana.

Kuma kungiyar al shebab ta fito ta yi ikirarin daukar alhakin kai harin inda aka kashe mayakanta hudu tare cafke guda.

Ahmed Badan, wani jami’in ‘Yan Sanda a birnin Mogadishu ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewar maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi bayan tayar bam.

Gidan cin abincin da aka kai harin, yana kusa da bakin teku ne a birnin Mogadishu kuma yana daukar mutane da dama  musamman baki ‘yan kasashen waje da ‘yan kasuwa.

Kungiyar Al Shebaab ta dade tana kai hare hare a fadin kasar, kuma ko a karshen mako ta yi ikrarin kashe sojojin Kenya sama da 100.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.