Isa ga babban shafi
Kenya-Somalia

Kenya na binciken kisan Al-Shebaab a Somalia

Gwamnatin Kasar Kenya ta ce ta kaddamar da bincike a kasar Somalia dan gano gaskiya kan zargin da kungiyar Al Shebaab ta yi cewar ta kashe sama da 100 daga cikin su ta kuma kama wasu da dama a harin da ta kai sansanin kungiyar kasashen Afirka dake kasar.

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta REUTERS/Thomas Mukoya
Talla

Shugaban rundunar sojin kasar Samson Mwathethe ya bayyana kaddamar da binciken inda yake cewar sun yi shine dan gano inda sojojin suke, dan sanin nawa aka kashe, nawa kuma aka jikkata kana nawa suka bata.

Jami’in ya ce babu shakka sojojin su na fuskantar yan ta’addan Al Shebaab ba tare da Karin bayani kan abinda ya same su ba.

Sai dai sanarwar da kungiyar Al Shebaab tayi na nuna cewar Mujahidan ta sun kutsa kai sansanin sojin dake kudu maso yammacin Somalia ranar juma'ar da ta gabata, inda suka kashe sojojin Kenya sama da 100, suka kwashe tarin makamai da motoci kana suka yi awon gaba da wasu sojojin 12 da ran su.

Sojojin Kenya 150 a wannan sansanin dake El Adde, kuma 4 daga cikin su da suka samu raunuka sun isa Nairobi jiya dan samun magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.