Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane 30 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a Adamawa

Rahotanni daga jihar Adamawa a tarayyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 30 cikinsu har da wani DPO na ‘yan sanda, a lokacin wani fada aka yi tsakanin makiyaya da kuma mazauna wasu kauyuka 4 da ke karamar hukumar mulkin Girei da ke jihar.

Taswirar Najeriya
Taswirar Najeriya The Long War Journal
Talla

Bayanai na nuni da cewa tun da asubar yau ne wasu da ake zaton makiyaye ne suka afka wa garuruwan Demsare, Wuna-mokoh, Dikajam da kuma Taboungo a wani abu da ake kallo a matsayin harin daukar fansa, lura da wani rikicin da ya taba faruwa tsakanin bangarorin biyu a baya.

To sai dai a lokacin da aka tura jami’an tsaro domin kwantar da rikicin, wasu da ake zargin cewa makiyayan ne sun kashe ‘yan sanda cikinsu har da DPO yankin mai suna Okozie Okereofor.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.