Isa ga babban shafi
Cameroun

Sama da mutane 30 suka mutu a harin Kamaru

Kimanin mutane 32 aka tabbatar da mutuwarsu a jerin hare haren kunar bakin wake da aka kai a wata kasuwa a yankin arewacin Kamaru a ranar Litinin inda mahukuntan kasar ke dara alhakin harin akan ‘Yan kungiyar Boko Haram.

Bayan harin Boko Haram a garin Marwa a Kamarou
Bayan harin Boko Haram a garin Marwa a Kamarou AFP PHOTO/STRINGER
Talla

'Yan kunar bakin waken sun tayar da bama baman ne a kofar shiga kasuwar garin Bodo da ke arewacin Kamaru, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin 32, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.

Sama da mutane 80 ne kuma suka jikkata a hare haren.

Majiyoyin tsaro a yankin sun ce maharan sun tarwatsa kansu ne a daidai lokacin da jama’a suka fara kwarara zuwa kasuwar, lamarin da ya sa ake fargabar adadin mamatan zai iya zarce yawan wadanda aka ruwaito tun da farko.

01:33

Adadin Wadanda suka mutu a harin Kamaru ya kai mutane 32

Kamaru na ci gaba da fuskantar barazana daga mayakan kungiyar Boko Haram da suka addabi kasar da hare haren kunar bakin wake.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.