Namijin Damisa ya sa an rufe makarantu a India
Hukumomi a yankin Bangalore na kasar India, yau Alhamis sun umarci a rufe makarantu kusan 130 bayan hango wani Namijin Damisa na yawo a yankin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wasu da suka hango Damisan na cewa akan idanunsu yana yawon neman abinci.
Hukumomin yankin sun nemi kowa ya zauna a gida saboda fargaban kada su gamu da Namijin Damisan.
Gwanayen tunkarar irin wadannan dabbobi dawa sun ce sun shafe sa’o’I da dama suna kokarin kame Damisan.
Rahotanni sun ce mutane 5 suka jikkata a kokarin kame Naman dawan. Amma Sai da aka shafe sa’o’I hudu kafin a samu nasarar cafke Namijin Damisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu