Isa ga babban shafi
Uganda

Yoweri Museveni ya lashe zaben Shugaban kasar Uganda

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya lashe zaben Shugabancin kasar, inda yanzu haka zai zarce da karin shekaru biyar sabon wa'adin mulkinsa, bayan da ya shafe shekaru 30 yana rike da iko.Madugun ‘yan adawa Kizza Besigye dake cikin takaran ya sa kafa ya shure sakamakon zaben saboda zargin an tafka magudi. 

Shugaban  Uganda Yoweri Museveni
Shugaban Uganda Yoweri Museveni rfi
Talla

A sako daya bayar daga inda ake tsare dashi, Kizza Besigye yace sam jama'a kada su amince da sakamakon zaben.

Yace muddin aka amince da zaben to kuwa an amince da take hakkin bil’adama kenan.

Shugaba Yoweri Museveni, mai shekaru 71 ya sami kashi sittin daga cikin dari na yawan kuri'u da aka jefa.

Kizza Besigye, mai shekaru 59 ya kasance sau hudu ke nan yana takara domin kawar da Shugaban nasu daga madafun iko.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.