Isa ga babban shafi
uganda

Bankin duniya ya soke tallafinsa a Uganda saboda mata

Bankin duniya ya soke aikin samar da kayayyakin more rayuwa na dalar Amurka miliyan 265 da ya dauki nauyi a kasar Uganda, bayan wani bincike ya nuna cewa ‘yan kwangilar gwamnati na cin zarafin kananan yara mata ta hanyar lalata da su.

Shugaban bankin duniya Jim Yong Kim
Shugaban bankin duniya Jim Yong Kim REUTERS/Gary Cameron
Talla

Tun a shekara ta 2009 aka fara gudanar da ayyukan na samar da kayayyakin more rayuwa ga al-ummar Uganda, wadanda suka hada da gina wata hanya mai tsawon kilomita 225 yayin da a tashin farko, bankin ya ware dala miliyan 190 kafin daga bisa ya amince da sake bayar da dala miliyan 75 a shekara ta 2011.

Wata sanarwa da shugaban bankin ya fitar, Jim Yong, ta bayyana cewa a watan Satumban da ya wuce, aka bukaci bankin da ya gudanar da bincike sakamakon korafe korafen da mutanen da abin ya shafa suka yi akan cin zarafin ‘yan matan.

To saidai sanarwar ba ta ambaci sunayen kamfanoni ko kuma mutanen da aka ce sun aikata laifin ba.

Shugaban bankin ya kara da cewa aikin samar da kayayyakin more rayuwar ya samu koma baya matuka kuma ya ce, dole ne su kare mutuncin talakawa da masu rauni a ayyukansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.