Isa ga babban shafi
Nijar

‘Yan Nijar na jiran sakamakon zabe

Al’ummar Nijar na dakun sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘Yan majalisu da aka gudanar a ranar Lahadi a yayin da a yau Litinin ake ci gaba da zaben a wasu yankunan kasar da ba a samu an yi zaben ba a jiya.

Ana tattara sakamakon zaben Shugaban kasa da na 'Yan Majalisu a Nijar.
Ana tattara sakamakon zaben Shugaban kasa da na 'Yan Majalisu a Nijar. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Tuni aka soma kidayar kuri’un zaben inda Shugaba mai ci Mahamadou Issoufou da ke neman wa’adi na biyu ya yi alkawalin samun nasara tun a zagayen farko.

Sai dai ‘Yan adawa sun soki hukumar zaben kasar da gazawa musamman na rashin kai kayan zabe a yankunan kasar da ya sa aka shiga kwana na biyu ana zabe.

Ana dai sa ran samun cikakken sakamakon zaben kwanaki biyar amma yanzu za a iya samun tsaiku saboda rashin gudanar da zaben a wasu yankunan.

Yankunan da ake gudanar da zaben a yau Litinin sun hada da wasu yankunan Jihar Tahoua, inda shugaba Mahamadou Issoufou ke da magoya baya, da kuma yankin Agadez da wani yanki na Zinder da Diffa da Tillaberi.

‘Yan takara 15 ne ke fafatawa a zaben ciki har da shugaba Mahamadou Issoufou da tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane da tsoffin Firaminista biyu Saini Oumarou da Hama Amadou.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.