A maido da kudade don biyan bukatun marasa lafiya
Ministan lafiya na kasar Libya, na bangaren gwamnatin da kasashen duniya suka yi na’am dasu, ya nemi Majalisar Dinkin Duniya da ta bari su yi amfani da kudaden kasar da aka boye a asusun bankuna a wajen kasar
Wallafawa ranar:
Ministan lafiya Redha El-Oakley ya shedawa manema labarai a Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Tunis, cewar abin babu dadi yadda kasar ke fama da matsalar rashin kudi da zata sayo magunguna don baiwa dimbin marasa lafiya, duk da cewa akwai kudaden ta masu yawa da aka hanata dake waje.
A kasar Tunisia kawai inji shi, akwai kudin kasar dala Miliyan 295 da aka rufe, kuma shekara daya kenan suna ta zarya zuwa Tunis amma samun kudaden ya faskara.
Libya ta fada cikin rikici ne a shekara ta 2011 a lokacin da aka kawo karshen mulkin marigayi shugaba Moammar Ghadafi
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu