Isa ga babban shafi
Congo

'Yan adawar Congo sun kafa hukumar zabe ta kansu

‘Yan takara biyar da ke neman shugabancin kasar Congo Brazzaville daga bangaren adawa, sun sanar da kafa ta su hukumar zabe mai zaman kanta, domin nuna adawa da hukumar zaben kasar wadda suke zargi da mara wa shugaba Sassou Ngesso baya.

Shugaban kasar Congo Brazaville, Denis Sassou Nguesso
Shugaban kasar Congo Brazaville, Denis Sassou Nguesso AFP
Talla

A karkashin wannan hukumar zabe, masu adawa da shugaba Denis Sassou Nguesso a zaben wanda za a yi a ranar 20 ga wannan wata, sun fitar da alkaluma na yawan wadanda suka cancanci jefa kuri’a da kuma adadin rumfunan zabe da suka sha bam bam da wanda hukumar zaben kasar ta sanar.

Ba a nan hukumar zaben ta ‘yan adawa za ta tsaya ba kamar dai yadda mai magana da yawunta Charles Bowao ya tabbatar, domin hatta a ranar zabe suna fatan kasancewa a cikin rumfunan kada kuri’a domin su shaidi yadda jama’a ke zabe.

Charles ya ce kafin ranar litinin ta makon gobe, za su dauki malaman zabe akalla dubu 5 da 300 wadanda za su tafiyar da aikin zabe a ranar 20 ga wannan wata da suna 'yan adawa.

To sai dai da aka tambayi kakakin ‘yan adawar ko daga karshe za su fitar da sakamakon zaben ne ko kuma a’a, sai ya amsa yana cewa, za su saurari irin sakamakon da hukumar zaben ta gwamnati za ta fitar domin jin ko ya dace da abinda ke hannunsu, daga nan kuma sai su dauki matakin da suke ganin cewa ya dace.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.