Isa ga babban shafi
Najeria

Boko Haram ta sace mata 16 a jahar Adamawa

Yanzu haka jami’an tsaro na ci gaba da kokarin gano wasu mata 16 da aka ce magoya bayan kungiyar Boko Haram ne suka yi awun gaba da su a Sabon Gari da ke cikin karamar hukumar Madagali da ke cikin jihar Adamawa. 

Iyayen 'Yan matan sakadaren Chibok da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa dasu a baya
Iyayen 'Yan matan sakadaren Chibok da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa dasu a baya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Bayanai sun ce an sace matan 16 ne lokacin da suka shiga jeji domin neman itacen girki.

Dan Majalisar wakilan Yankin Adamu Kamale ya tabbatar da labarin ga kafar Premium Times, yayin da kakakin Yan Sandan Jihar Othman Abubakar yace sun tura jami’an tsaro dan ceto matan.

Wannan dai bashi bane karon farko da Kungiyar ke garkuwa da mutane musanman mata, a akwai wasu yan matan makarantar kwanan Sakandaren garin Chibok na Jahar Borno sama da 200 da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa dasu shekaru 2 da suka gabata kuma har ya zuwa wannan lokacin ba amo ba labari.

A yau dinnan aka wayi gari da ganin wani sabon faifan bidiyo wanda shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar inda ya yi bayani cikin murya tattausa sabanin yadda ya saba yi a baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.