Ana Tsare da Jagoran Adawa Na Kasar Gambia
Jagorar babbar jam'iyyar adawa a kasar Gambia, Ousainou Darboe na tsare hannun jami'an tsaron kasar tun jiya Asabar, sakamakon wani bore karo na biyu da sukayi suna bukatar dalilan kisan wani dan siyasa.
Wallafawa ranar:
Mousainou Darboe, wanda lawyen kare hakkiin bil'adama ne kuma shugaban jam'iyyar adawa ta United Democratic Party, UDP, a takaice, ‘yan sanda suka tafi dashi tare da wasu mutane uku jim kadan da suka fara jerin gwano daga gidansa a bayan garin birnin Banjul.
Wasu ganau na cewa sai da ‘yan sanda suka kori taron masu boren da hayaki mai sa kwalla kafin su fara kamen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu