Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

An ba Machar wa’adin karshe ya dawo Juba

Manyan kasashen duniya sun ba shugaban ‘Yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar wa’adin karshe daga nan zuwa Asabar ya dawo Juba babban birnin kasar bayan shafe lokaci ana jiran isowarsa domin tabbatar da gwamnatin hadin kai tsakanin shi da Salva Kiir.

Jagoran 'Yan tawaye a Sudan ta kudu Riek Machar
Jagoran 'Yan tawaye a Sudan ta kudu Riek Machar REUTERS
Talla

Majalisar Dinkin Duniya da hukumar da ke sa ido da tantacewa ta duniya na fargaba akan rashin isowar Machar fadar gwamnatin Sudan ta Kudu babbar barazana ce ga tabbatar da zaman lafiya a jinjirar kasar.

Sai dai rahotanni sun ce Magoya bayan shugaban ‘yan tawaye sama da 100 ne suka isa birnin Juba a yayin da ake dakon isowar jagoran a karon farko a tsawon shekaru biyu

Kakakin shugaban ‘yan tawayen William Ezekiel yace babu shakka Riek Machar zai karaso nan ba da jimawa ba jim kadan da sauke wasu magoya bayan Machar da yawansu ya kai 125.

Mista Ezekiel ya ce yanzu haka ana kan isowa da wasu manyan magoya bayan Machar daga shalkwatar 'yan tawaye da ke kan iyakar kasar Habasha.

Jagoran 'yan adawa na Sudan ta Kudu Riek Machar zai dawo kasar ne don aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnati da 'yan tawaye, inda Machar zai karbi sabon mukaminsa na mataimakin shugaban kasa kamar yadda yarjejeniyar ta shata.

Shekaru biyu ke nan rabon jagoran yan tawayen ya sa kafa a birnin Juba tun bayan rikicin da ya barke a tsakanin shi shugaba Salva Kiir, rikicin da ya rikice ya koma yakin basasa tare da haddasa asarar rayukan dubban mutane baya ga miliyoyi da suka tsere daga muhallinsu dan tsanannin rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.