Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnati za ta fara daukar matasa aiki

Gwamnatin Najeriya tace za ta soma shirin samar da ayyukan yi na koyarwa ga ‘yan kasar 500,000 daga ranar 12 ga watan Yuni. Shirin ya shafi matasa da suka kammala karatun Jami’a amma ba aiki.

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo REUTERS
Talla

A cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar daga ofishin Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ta bukaci matasan da ba su da aikin yi su gaggauta shiga tsarin ta hanyar aika bukatarsu a shafin intanet npower.gov.ng.

Shirin dai na sa-kai kuma na wuccin gadi a wa’adin shekaru biyu da gwamnatin ta bullo da shi domin samarwa matasa madogara kafin su samu aiki na dindin.

Za a rika biyan Matasan albashin kudi Naira dubu ashirin da uku a wata, sannan za su samu horo da dubarun koyarwa da kuma samun na’urar Kwamfuta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.