Isa ga babban shafi
Nigeria

Shugaban Nigeria Ya Nemi 'Yan Kasar Da Su Kara Hakuri

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya yabawa ‘yan Nigeria saboda juriya da hadin kai da yake samu a tsawo shekara daya da yake kokarin maido da daraja da mutuncin kasar.  

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Talla

Shugaba Muhammadu Buhari na jawabi ne na musamman albarkacin cika shekara daya yana bisa madafun iko.

Ya ce a tsawon shekara daya an fuskanci matsaloli da dama gameda faduwar farashin man fetur, amma kuma zai ci gaba da bada himma don ganin an fita daga dimbin matsalolin da suka dabaibaye kasar.

Ya ce dukkan manyan kasashen da suka ci gaba saida suka dauki kwararan matakai da samun juriya daga jama’a kafin su kaiga nasara.

Muhammadu Buhari ya ce bayan an yi nasarar Koran ‘yan Kungiyar Boko Haram daga wuraren da suka kwace yanzu abinda ke gaban Gwamnati shine ganin mazauna yankunan da aka kwace sun sami komawa yankunan su.

Acewar Shugaban Gwamnati na duba yadda za'a bullo da tsari mai dadewa domin ganin an kawar da munanan dabiu a cikin harkokin Gwamnati
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.