Isa ga babban shafi
Senegal- Chad

An daukaka kara kan hukuncin Hissene Habre

Lauyoyin da kotu da dauka domin kare tsohon shugaban Chadi Hissene Habre, sun daukaka kara kan hukuncin da aka yanke ma sa na daurin rai da rai, bayan an same shi da aikata laifukan yaki da kuma cin zarafin al’umma a lokacin da ya ke rike da madafun iko.

Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre
Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre © .AFP/Stringer
Talla

Daya daga cikin lauyoyin Mbaye Sene ya ce, a jiya jumma’a suka daukaka karar domin kalubalantar hukuncin wanda wata kotun Senegal ta yanke a ranar 30 ga watan Mayun daya gabata.

Sai dai ana zaton har nan da watan Aprilun badi, lauyoyin ba za su iya kammala abubuwan da ake bukata ba dangane da daukaka karar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.