Isa ga babban shafi
Senegal- Chad

Hissene Habre ya daukaka kara

Tsohon Shugaban kasar Chadi Hissene Habre ya daukaka kara domin kalubalantar hukuncin daurin rai da rai da Kotun ta Musamman a Dakar ta zartar bayan samun shi da laifin cin zarafin Bil Adama a lokacin da ya ke mulkin Chadi.

Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre
Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre © .AFP/Stringer
Talla

Mai magana da yawun kotun da ta daure Habre a Senegal, Marcel Mendy ya ce lauyoyin Habre sun gabatar da takardunsu na daukaka karar, kuma kotun za ta nada alkalan da za su duba kokensu.

Wannan shari’a ita ce irinta ta farko da wata kotu a wata kasa ta daure tsohon shugaban wata kasa.

Tsohon Shugaban na Chadi ya ki  magana a kotun da ake shiga da shi da karfin tuwo a tsawon watanni 10 da aka shafe ana shari'ar.

Sama da mutane 40,000 aka kiyasta an kashe da wasu da aka yi garkuwa da su da kuma mata da aka yi wa fyade zamanin mulkin Habre tsakanin 1982 zuwa 1990.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.