Isa ga babban shafi
Najeriya

An bayar da lasisin shigo da nau’in abincin da aka sauya wa halitta a Najeriya

Wata Kungiya da ake kira Global Profile Alliance da ke Najeriya ta bukaci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ya binciki hukumar National Biosafety Management da ta bayar da lasisin amfani da abincin da aka sauyawa halitta a kasar ba tare da la’akari da illar shi ba.

Irin Masarar da aka sauya wa halitta na haifar da cututtukan da suka shafi koda saboda sinadarin da suke dauke da shi.
Irin Masarar da aka sauya wa halitta na haifar da cututtukan da suka shafi koda saboda sinadarin da suke dauke da shi. fothergills
Talla

Shugaban kungiyar Philip Njemanze ya koka kan yadda hukumar ta yi gaban kanta wajen bayar da lasisin shiga da masarar da aka sauyawa halitta kasar duk da sanin matsalar da ya ke haifarwa.

Jami’in ya kawo misali da kasashen Faransa da Jamus da Poland da Italia da Austria wadanda suka haramta shiga da irin masarar kasar su saboda sannin illar da ta ke yi.

Njemanze ya ce wani masanin kimiya a Faransa Gilles-Eric Seralini ya gudanar da binciken da ya tabbatar da cewar irin wannan Masara na haifar da cututtukan da suka shafi koda saboda sinadarin da suke dauke da shi.

Shugaban kungiyar ya kuma ce abin mamaki ita hukumar Najeriya ta bayar da lasisin ne ranar 30 ga watan jiya wanda kuma ranar hutu ce a Najeriya, abin da ke nuna cewar akwai rashin gasiya cikin lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.