Isa ga babban shafi
WHO

Hukumar Lafiya za ta gana kan annobar zazzabin shawara

Hukumar lafiya ta Duniya ta shirya gudanar da taron gaggawa don gano hanyar dakile annobar zazzabin shawara da ta kunno kai a kasar Angola, ganin barazanar da cutar ka iya yi ga lafiyar sauran al’ummar duniya.

Kalilan daga cikin al’ummar yankin Afrika ne suka damu da yin  allurar rigakafin cutar shawarar
Kalilan daga cikin al’ummar yankin Afrika ne suka damu da yin allurar rigakafin cutar shawarar Daniel Becerril/Reuters
Talla

A jibi alkhamis ne hukumar lafiya ta Duniya wato WHO ta shirya zaman tattauna hanyar magance annobar cutar shawarar da ta riga ta hallaka mutane sama da 200 a kasar Angola, alkaluma da hukumomin kasar suka fitar na cewa mutane 2,267 ne suka kamu da zazzabin tun bayan bullarta a watan Disanbar data gabata.

Hakazalika mutane sama da 44 sun kamu da cutar a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo

A kasar Uganda kuwa an sami mutanen dake fama da shawarar kuma duk wadannan mutanen wadanda aka tabbatar sun dawo kasar ne daga Angola.

A kasar Chana an gano wasu mutane 11 dake fama da shawarar bayan sun dawo daga Angola.

Sakamakon Wadannan binciken ne ya harzuka Hukumar Lafiyar gaggauta zama don daukar matakan dakile yaduwar cutar gudun aukuwar halin da aka fada bisa a yayin annobar Ebola da aka zargi Hukumar da jan kafa.

Kalilan daga cikin al’ummar yankin Afrika ne suka damu da yin allurar rigakafin cutar shawarar duk da ingancinsa inji Hukumar.

Hukumar lafiya tace ta aika da allurar riga kafin zazzabin da ya zarta miliyan biyu zuwa Angola da Jamhuriyar Demokradiyar Kongo a kokarin dakile shawarar, ganin cutar ka iya zama babbar barazana ga kiwon lafiyar sauran al’umma a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.