Isa ga babban shafi
Angola

Mutane sun kamu da zazzabin shawara a Angola

Mutane 99 zazzabin shawara ta hallaka a cikin watanni biyu da suka wuce a kasar Angola sakamakon barkewar cutar wadda ta kama mutane 462.Hukumomin kasar sun sanar da dauka tsauraren matakan da suka dace domin wannan wannan bala'i cikin dan karamin lokaci. 

Sauro dake haifar da zazzabin Shawara  a kasar Angola
Sauro dake haifar da zazzabin Shawara a kasar Angola DR
Talla

Cibiyar yaki da cututtuka dake Luanda babban birni kasar ta sanar da cewar daga cikin mutane 173 da suka kamu da zazzabin shawara a unguwar Viana 73 sun mutu.
Yanzu haka hukumomin kasar sun kaddamar da aikin rigakafi dan dakile cutar.
Kasar Angola na daga cikin kasashen Afrika da aka fi samu mutuwar mutane bayan kamuwa da zazzabin shawara .
cutar da aka ce sauro ke yadawa.

Alamomin cutar sun hada da ciwon kai da amai da kasala kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar.

Yanzu haka dai an yi nasarar yiwa mutane sama da 450,000 riga-kafi yawanci a Luanda babban birnin kasar inda aka fi samun yawan wadanda ke dauke da kwayar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.