Mamata sun karu a ambaliyar Ruwan Angola
Mutane 64 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon ambaliyar Ruwa da ta samo asali daga Ruwan sama masu matsanancin karfi da aka shatata a yankin yammacin kasar Angola
Wallafawa ranar:
Asarin wadanda suka mutu dai an same su ne a birnin Lobito da ke a gabar Ruwan Lardin Benguela, daga cikinsu kuma, akwai yara kanana 35.
Ambaliyar Ruwan kuma ta zo wa mutanen ne suna bacci da tsakiyar Dare, kuma Ruwan da aka yi da karfin gaske ya lalata gidaje da dama, abinda aka ce shi ne musabbabin mutuwar mutane da dama.
Shugaban kasar ta Angola Jose Eduardo dos Santo, ya yi alwashin taimakawa mutanen da hatsarin ya shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu