Isa ga babban shafi
CAN 2013

Afrika ta Kudu ta tsallaka zuwa zagaye na biyu, Cape Verde ta doke Angola 2-1

A cigaba da gasar cin kofin Nahiyar Afrika, masu masaukin baki, wato Afrika ta Kudu sun fitar da kasar Morocco daga gasar bayan sun ta shi a wasan da ci 2-2A yayin da wasa tsakanin Angola da Cape Verde aka tashi da ci 2-1, inda Cape Verde ta yi nasara akan Angola.  

Dan wasan Afrika ta Kudu, Thabo Matlaba a lokacin da suke karawa da Algeria
Dan wasan Afrika ta Kudu, Thabo Matlaba a lokacin da suke karawa da Algeria REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

A rukuni na biyu kuwa, a yau dai Janhuriyar Demokradiyar Congo zata kara da Mali, a yayin da Niger kuma zata fafata da Ghana.

A gobe Burkino Faso zata kara da Zambia kana Najeriya ta kara da Ethiopia ko kuma kasar Habasha.

Najeriya dai na da zabi biyu, ko ta yi kokari ta yi nasarar wasanta da Ethiopia, ko kuma ta nemi yin canjaras, sannan baya ga haka ta yi fatan Burkina Faso ta doke Zambia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.