Isa ga babban shafi
CAF

Yaya Toure ne Gwarzon Afrika

Dan kasar Cote d’Ivoire Yaya Toure na Manchester City shi ne ya lashe kyautar Gwarzon Afrika na bana bayan ya samu rinjayen kuri’u fiye da dan uwansa Didier Drgoba da kuma Alexandre Song na Kamaru. ‘Yar wasan Equatorial Guinea Genoveva Anoman ita ce aka ba Jarumar Afrika a bana.

Dan wasan Manchester City Yaya Toure  na Cote d'Voire yana jawabi kusa da matarsa tare Drogba a gefe bayan lashe kyautar gwarzon Afrika.
Dan wasan Manchester City Yaya Toure na Cote d'Voire yana jawabi kusa da matarsa tare Drogba a gefe bayan lashe kyautar gwarzon Afrika. REUTERS/Luc Gnago
Talla

Toure mai shekaru 29, karo na biyu ke nan a jere yana lashe kyautar bayan ya taimakawa Kungiyar Manchester City lashe kofin Premier karo na farko a shekaru 44 da suka gabata.

A yanzu dai Yaya Toure ya shiga sahun su Drogba da suka lashe kyautar karo na biyu inda suke neman kamo kafar Samuel Eto’o na kamaru wanda ya lashe kyautar gwarzon Afrika sau hudu.

Zambia ce dai ta lashe kungiyar Afrika ta bana, saboda ta lashe kofin Afrika bayan doke Cote d’Ivoire a wasan karshe da aka gudanar a kasashen Gabon Eqautorial Guinea. Kuma kocin Zambia ne aka ba Gwarzon koci a Afrika.

A bangaren mata kuma ‘Yar wasan Eqautorial Guinea Genoveva Anoman ita ce aka ba jarumar Afrika a bana bayan ta zira kwallaye 6 a raga a gasar matan Afrika.

Kungiyar Al Ahly ta Masar kuma ita ce kungiyar Hukumar CAF bayan lashe kofin Zakarun Afrika karo na bakwai a bana. Kuma Dan wasan Al Ahly Mohamed Abourtreika shi ne ya lashe gwarzon dan wasa mai taka leda a gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.