Isra'ila Na Bukatar Kujeran 'Yar Kallo cikin Kungiyar Tarayyar Afrika
Fira Ministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya bayyana goyon bayan kasar sa ga bukatar takwaran sa na kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu na baiwa kasar kujeran 'yar kallon cikin kungiyar Tarayyar Africa.
Wallafawa ranar:
Acewar Fira Ministan kasar Habasha, Israila ta chanchanci matsayin saboda irin gudunmawa da take bayar wa ga kasashe da yawa a Africa.
Fira Ministan Habasha na Magana ne yayin da yake karban bakuncin Benjamin Netanyahu a birnin Addis Ababa.
Fira Ministan Isra'ila na rangadin kasashen Africa hudu ne.
Kungiyar Tarayyar Africa kan bada gurbin zama ‘yar kallo ga kasa wadda ba cikin nahiyar Africa take ba.
A birnin Addis Ababa ake da cibiyar kungiyar Tarayyar Africa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu