Majalisar Dinkin Duniya tace yan kasar Sudan ta kudu 37,000 yanzu haka suka tsallaka zuwa kasar Uganda dan samun mafaka daga tashe tashen, hankula da kokawar mulkin da ake tsakanin shugaban kasa Salva Kiir da shugaban Yan Tawaye Riek Machar.
Hukumar kula da Yan gudun hijira ta Majalisar tace a cikin makwanni uku da suka gabata an samu kwararar Yan gudun hijirar da ba’a taba samu ba a cikin watanni 6 da suka gabata, kuma akasarin su mata ne da yara kanana.
Farfesa Dandatti Abdulkadir tsohon Jakadan Najeriya a Libay ya yi tsokaci a zantawarsu da Bashir Ibrahim Idris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu