Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Dakarun Riek Machar sun fice daga Juba

Mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudu kuma jagoran ‘yan tawaye ya fice da dakarunsa daga Juba babban birnin kasar, yayin da aka shiga kwana na uku na tsagaita wuta tsakaninsu da dakarun gwamnati.

Dakarun mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar sun fice daga birnin Juba
Dakarun mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Riek Machar sun fice daga birnin Juba ALBERT GONZALEZ FARRAN / AFP
Talla

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin sake barkewar wani rikici a juba bayan shafe kwanaki biyar ana barin wuta tsakanin dakarun Riek Machar da na shugaba Salva Kiir.
 

Kakakin Riek Machar ya tabbatar da ficewar dakarunsu daga Juba bayan tsagaita wuta da bangarorin biyu suka yi.

Akwai dai ‘yan tawayen da shugaba Salva Kiir ya yi alkawarin yi masu afuwa wanda suka jagoranci musayar wutar da aka yi da dakaurnsa a Juba.

Sai dai majalisar dinkin duniya ta bayyana fargabar yiyuwar barkewar wani sabon rikici tsakanin dakarun da ke biyayya ga mataimakin shugaban kasa Reik Mashar da kuma masu biyayya ga shugaba Salva Kiir wadanda suka shafe kwanaki biyar suna barin wuta.

Amma Gatdet Dak da ke magana da yawun Reik Machar ya ce sun fice da dakarunsu daga Juba domin guje wa sake barkewar rikici a kasar.

Sannan ya ce shugaban na ‘yan tawaye kuma mataimakin shugaban kasa zai bar juba na wani lokaci har sai komi ya lafa.

Dubban mutanen Sudan ta kudu ne dai ke tsere wa kasar zuwa Uganda, yayin da ‘yan kasashen waje da dama ke neman hanyar ficewa daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.