Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta dakatar da kafofin BBC da VOA na tsawon makwanni biyu

Hukumomin Burkina Faso sun dakatar da kafofin yada labaran BBC da na Muryar Amurka, daga watsa shirye-shiryen na tsawon makwanni biyu, saboda watsa rahoton zagin take hakkin bil adama da ke ake yi wa sojojin kasar.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan.
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan. © AFP
Talla

A jiya alhami ne dai kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, ta ce sojojin Burkina Faso sun kai harin ramuwar gayya yankin Arewacin kasar, inda suka kashe fararen hula 223 ciki kuwa har da kananan yara 56.

A cikin sanarwar da hukumar kula kafofin yada labaran kasar ta fitar, ta ce ta dauki matakin dakatar da kafafen BBC Afrika da VOA ne, bayan wallafa labarai a kafofin sadarwarsu na zamani, da ya zargi sojojin kasar da take hakkin bil adama.

Hukumar ta ce rahoton kafofin yada labaran, na tattare da rashin adalci ga sojojin Burkina Faso bisa zargin da aka yi musu.

Tun a shekarar 2015 ne Burkina Faso da Mali da ke yammacin Afrika, ke fuskantar kalubalen hare-haren masu ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.