Isa ga babban shafi

Sojojin Burkina Faso sun yi wa fararen hula 223 kisan gilla - Rahoto

Wani sabon rahoton kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ya bankado yadda Sojojin Burkina Faso suka yiwa fararen hula akalla 223 kisan gilla ciki har da kananan yara da kuma jariri a yankin arewacin kasar.

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso © AFP
Talla

Rahoton na HRW ya ce tun farko Sojojin na Burkina Faso sun zargi mutanen kauyen Nondin da Soro da taimakawa ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare sassan kasar dalilin da ya sanya yi musu kisan gillan bayan kai sumame kauyen a ranar 25 ga watan Fabarairun da ya gabata.

Rahoton ya ce cikin mutanen 223 da Sojin na Burkina suka kashe har da kananan yara da 56 baya ga jariri kuma galibinsu an hada da iyayensu yayin kisan.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Afrika su shiga cikin batun don gudanar da bincike tare da hukunta masu hannu a kashe-kashen.

Rahoton na HRW shi ke matsayin zargi na baya-bayan da aka yiwa Sojin na Burkina Faso kan kisan fararen hular da basu ji ba basu gani ba.

HRW ta ce Sojojin na Burkina Faso sun kashe al’ummar garuruwan na Nondin da Soro ne kadai akan zargi ba tare da hujjar da ke tabbatar da hannunsu wajen taimakawa ‘yan tadda ba, musamman kananan yara da kuma jarirai akalla 56 da kisan ya rutsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.